BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da hudu
Shin dan Zina zai shiga Aljanna idan ya yi aiki na kwarai?
SHAIKH ZAKZAKY: To lalle ba inda aka kawo maganar cewa dan zina ba zai shiga Aljanna ba, ba a taba kawo wannan maganar ba. Kuma shi dan zina, kamar yadda ya zo cewa wata rai ba ta daukar alhakin wata, shi ya sami kansa ne kamar yadda ma dan halas ya sami kansa, ba a dora masa ba, sai dai saboda kiyaye mutunci a kan guji ba shi wadansu matsayi kamar na Limanci ko shugabanci, don akwai aibun wannan laifi wanda ake ganin sa da shi.
TAMBAYA: Shin ya halatta musulmi ya ci abincin kiristoci ko kiristimeti ko kuma na murnar sabuwar shekara (New year)?
Daga Yahya Unguwar Dambuwa Potiskum Jihar Yobe.
SHAIKH ZAKZAKY: To, na'am idan ba an damrafa shi da ibadar wanin Allah bane, kuma ya inganta ya ci din. Wato in abincin wanda ya inganta a ci ne, sannan kuma ba a ganin yana da dangantaka da bautar wanin Allah, to ba komai.
TAMBAYA: Shin menene hukuncin irin rubuta sunan Allah da ake yi a jikin bodin manyan motoci na dibar kaya, kuma har jama'a na tabawa a duk lokacin da za su hau motar?
Daga Idris Haruna Dagauda, Jihar Bauci.
SHAIKH ZAKZAKY: To, wannan rashin girmama sunan Allah ne, bai kamata mutum ya sa sunan Allah a wuraren da yake za su iya saduwa da kazanta ba, ko kuma wadanda suke ba musulmi ba su rinka tabawa ba.
TAMBAYA: Ko ya halatta uba ya biya kudin zance na 'yarsa idan mai nemanta da aure ya bukaci haka idan ba a yi auren da shi ba?
Daga Idris Haruna Dagauda, Jihar Bauci.
SHAIKH ZAKZAKY: To ,lallai ban san wani kudin zance ba. Abin da aka sani shi ne kawai akan ba da sadaki ne, kuma in ba a daura aure ba, ka ga sai a ba shi sadakinsa kenan. Amma irin kyaututtukan da yake bayarwa irin na yau da kullum, to, ana daukarsu tamkar yana ba ta ne shi da ita, ba a daukarsa a matsayin sunansa sadaki ne. Sai dai al'adun wasu idan sun sa masa ka'ida cewa in har za su ba shi auren, sai ya biya wani abu, to, sai ya biya, sai ba su ba shi ba, to za su ba shi kayansa.
TAMBAYA: Ina hukuncin wanda ya yi sahur ko bude baki da kayan haram, kamar kayan maye ko na sata?
SHAIKH ZAKZAKY: To ya aikata haramun ne, sai dai ya fi tsanani tunda yake inda aka fi bukatar ya yi da halas ne ya yi da haram.
Amma ba za mu ce wai ba shi da azumi ba, sai dai ya aikata babban laifi. Musamman idan watan azumin Ramadana ne, kamar yadda ake nunka lada, ana nunka zunubi. Sai dai idan da a ce ya karya azumin ne da dayan wadannan, to, shi ana gallaza masa kaffara, ana yi masa 'double.' Idan mutum ya na azumin watan Ramadana ne ya sha giya da rana, to kaffara biyu zai yi. Haka zalika idan ya yi zina da rana, to shi ma ana nunka masa kaffara ne. Wato maimakon azumin kwana sittin, ana so ya yi dari da ashirin kenan a jere.
TAMBAYA: Meye hukuncin wanda ya bar kasar nan da yamma yana azumi, amma ya je wata kasa ya tarar can tsakar rana ce, ko ya bar kasar nan da rana ya je can ya tarar da magariba ta yi. Kuma yaya zai yi da salla idan har tafiyan tasa ba ta kasaru bace?
SHAIKH ZAKZAKY: To, lalle ba yadda za a ya ya yi tafiyar da ba ta kasaru ba har ya je ya samu rana ta canja matsayinta kamar yadda shi ya ambata. Domin kuwa kafin a sami bambancin rana irin wannan, lalle tafiyar dole za ta kai mikidarin tafiyar fiye da awa guda ma a sama kafin ya je, wanda yake kuma tilas ya wuce mikidarin kasaru, sai dai abin da za mu iya ce masa shi ne; Na farko dai ba yadda za yi a tafiyar nan da ya ambata ta zama ba ta kai mikidarin kasaru ba. To, saboda zon din lokaci, bambancin awa-awa ne yake da shi, to, kuma ga bayanin nan da ya yi, to dole ma zon din ma ya nuna ya ma wuce awa guda, kuma ya nuna tafiyar nan lalle ta sama ya yi, ba yadda za a yi ya yi tafiya ta sama na fiye da awa guda, sannan ya zama kasaru ba ta kama shi ba. Saboda haka lazim kasaru ta kama shi, kuma tun da kasaru ta kama shi, to babu maganar azumi tunda azumi ya ma haramta masa ya yi, sai dai batun salla. Sai mu ce ita salla ita ce idan ya ma yi yanzun, mukaddara ya yi magriba da isha, sai kuma ya tafi wani gari sai ya ga da rana, rana ba ta fada ba, to in ta fada zai sake yin magriba da isha.
TAMBAYA: Shin ya halatta mutum ya dauke mace a kan mashin din aceba?
SHAIKH ZAKZAKY: To, mun sha amsa wannan, mun bayyana cewa hada jiki da wadda take ba muharrama ba, bai halatta ba.
TAMBAYA: Shin ya halatta irin zaman da mata da maza suke ya a cikin motar haya?
SHAIKH ZAKZAKY: To, shi ma dai kamar amsar na babur ne, ba bambanci. Bai halatta namiji da mace jikinsu ya hadu ba alhali ba matarsa ba, ko muharraman juna ne ba.
TAMBAYA: Ko ya halatta mutun ya hada mazhabobi biyu yana aiki da su kamar ya yi alwala da wannan, ya yi salla da wannan?
SHAIKH ZAKZAKY: Lalle mu a wurinmu akwai masu ijjtihadi wanda ake yin takalidi da su. Saboda haka sai ka duba yaya ijjtihadin wanda kake takalidi da shi, in har ka san ana yin takalidi din. Galibi dai yakan zama akwai 'Risala Amaliyya' da ake samu daga mujjtahidi din. To lalle ya duba shi 'Risala amaliyya' din mujjtahidin da yake takalidi da shi ya ga bayanin irin wannan.
TAMBAYA: Mutum ne musulmi, amma Mahaifiyarsa ba ta salla, ko idan ta mutu zai iya cin gadonta?
SHAIKH ZAKZAKY: Wata kila yana nufin ita ba musulma bace kenan, ba musulmar da ba ta salla ba, (domin ana iya samun musulmi ba ya salla), sai a ce masa ba ya salla, amma idan mutum ba musulmi ne ba, ana ce masa ba musulmi ne ba, ba ana ce wa ba ya salla bane. Saboda in bai musulunta ba, ko ya yi salla ma ai sallar ba ta inganta gare shi ba. In yana nufin ita ba musulma bace, kamar yadda na fahimta, to haka nan dai ya na da gadonta, musulmi yana gadon kafiri, kafiri ne ba ya gadon musulmi.
TAMBAYA: Ina so Malam ya yi mani bayani dangane da taba sigarida shake, wato 'Snuff,'domin wasu Malamai na ce wa haramun ne, yayin da wasu ke cewa bata da haramci?
Daga Muhammad Bindawa, Suleja Jihar Neja.
SHAIKH ZAKZAKY: To lalle kamar yadda ya ji din nan ne, fatawoyin Malamai ne daban-daban, wasu Malamai sun haramta. Saboda haka in kana takalidi da mujjtahidin da ya haramta, sai ka bari, in kuma ka aikata ka yi laifi. Wadanda kuma suka ce halas ne, shi kenan, ko da su ma na san ba sun ce halas ne kada'an ba, sun dan karfafa gwiwar mutane da su bari. Ala ayyi halin, wannan wani abu ne wanda yake ba wani taimako yake kawowa ko, ba kuma wani lada ake samu dangane da shi ba. Amma mutane sukan ji dadin suna yi, kuma wasu Malamai suna ganin tun da ba a rawaito akwai wani abin da ya hana ba, sun samu su yi haka. To dai ya rage maka, da wa kake ko yi, in kana koyi da Malamin da ya halatta ne, to ruwanka, in kuma da wanda ya halatta ne, sai ka bari.
TAMBAYA: Ko ya halatta Malami ya yi zaune yana karantarwa ba tare da wata sana'a ba, sai dai abin da almajiransa suka kawo masa?
SHAIKH ZAKZAKY: To wannan sai mu koma ga 'urfi,' bisa 'urfin' mutane yana iya samar mana da mafita dangane da wannan. Idan su mutane da ma haka suka saba, cewa shi Malami akan dauki dawainiyarsa ne, shi kuma ya zo yana ta karantarwa, to, wannan babu laifi da shi. Idan kuwa har zai zama yana wata sana'a ne, kuma yana koyarwa, ka ga kamar 'Part time' kenan yake yi. Don in zai hada sana'ar ciyar da kansa da kuma koyarwa, to lalle zai zama koyarwar baina-baina ne, ba dai koyarwa na ko da wane lokaci ba. Saboda haka wannan 'urfin' mutanen za ka koma ka gani ya suke yi. Ala ayyi halin dai, shi ne cewa ya halatta, tun da shi an hana masa wata sana'a kenan don ya shagalta da koyarwa.
TAMBAYA: Ni sana'ata fatanci daga Sakwato zuwa Lagos ko ya halatta in ci maganin tauri don gudun 'yan fashi da makami musamman ma 'yan gungume masu sara wa mutum adda?
Daga Abubakar M A Goronyo, na sashin nazarin harsunan Nijeriya da ke Kwalejin ilimi ta Sakkwato.
SHAIKH ZAKZAKY: To, lalle ban san menene tauri ba, tana iya yuwa wani nau'in abu ne wanda ya hada da wasu 'yan tsaface-tsaface da wadansu abubuwan da suka kauce wa hanya.
Amma da za a ce ainihin wani magani ne wanda yake 'dabi'i,' kamar a ce wata riga da take hana kurdawar harsashi, masalan, ko wani sulke da yake iya kare mutum daga saran wuka, to, za mu ce wannan wani abu ne da aka sani. Amma tauri ba a san shi ba. Saboda haka ba yadda zai a yi a yi hukunci da abin da ba a sani ba. Amma ya halatta ya kare kansa da abin da shari'a ta yarda da shi.
TAMBAYA: Mutum ne ya karbi bashi daga Hukumar samara da ayyukan yi ta kasa, shi kuma ya ba su takardun kammala makarantarsa, daga baya da ya sami aikin gwamnati bai kai masu kudinsu ba, kuma bai je ya karbi takardunsa ba, sai ya ci gaba da aikinsa har ya mutu. To menene matsayin wannan bashi ga magadansa.
Daga Abubakar M A Goronyo, na sashin nazarin harsunan Nijeriya da ke Kwalejin ilimi ta Sakkwato.
SHAIKH ZAKZAKY: Ai shi wannan zai kasance wani abu ne wanda aka yi yarjejeniya aka rubuta, yana da ka'ida na tabbatarwa. Ba haka kawai za ka karba ya zama shi kenan zance ya kare ba, su masu ba da bashin ba za su sake tuntubar sad da zai zama ya biya bashin ba, akwai wadansu matakai da ake dauka. Alahyyu halin in mutum ya mutu akwai bashi a kansa magidansa zai su biya.